Omoyele Sowore ya samu ‘yanci bayan kwana uku a tsare

0
14

Dan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, ya samu ‘yanci bayan shafe kwana uku yana tsare.

An tsare shi ne bayan amsa gayyatar ofishin rundunar ‘yan sanda a Abuja, lamarin da ya haddasa zanga-zanga a jihohi da dama.

Kafin kama shi, Sowore ya jagoranci zanga-zangar neman ingantacciyar walwala ga tsofaffin ‘yan sanda tare da sukar tsarin karin girma a rundunar.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here