Hukumar Shirya Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta sake duba sakamakon jarrabawar inda ta bayyana cewa kashi 62.96% na daliban da suka rubuta jarrabawar sun samu nasara a aƙalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Daga cikin dalibai 1,969,313 da suka rubuta jarrabawar, 1,239,884 ne suka ci darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi, karin kashi 24.68% idan aka kwatanta da 754,545 (kashi 38.32%) da aka sanar a baya.
WAEC ta danganta matsalar farko ta rashin cin jarrabawar da yawa ga kuskuren amfani da kundin lambobin sirri da ba daidai ba wajen buga takardar tambayoyin Turanci (paper 3). Hukumar ta ce wannan ya faru ne saboda wani tsarin da ta yi amfani da shi a wannan shekara a darussa huɗu, na Turanci, Biology, Economics, da Lissafi, don rage satar amsa.
Sakamakon farko ya jawo ƙorafe-ƙorafe daga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, musamman game da yawan rashin cin darasin Turanci. Wannan ne ya sa hukumar ta sake nazari kan sakamakon.
Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Amos Dangut, ya bayyana a taron manema labarai cewa an samu kuskuren buga takardun jarrabawar, wanda ya janyo matsalar da aka gani a sakamakon farko.