Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kano Ta Bukaci Jama’a Su Rinƙa Bayyana Mata Ƴan Sanda Masu Cin Hanci 

0
20

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bukaci al’umma da su rika kai rahoto kan duk wani ɗan sanda da ke karɓar cin hanci domin kare ko ɓoye laifukan masu aikata miyagun ayyuka a yankunansu.

Wannan kiran na zuwa ne biyo bayan bayyana wani bidiyo da wani matashi ya wallafa, inda ya zargi wasu jami’an ‘yan sanda a unguwar Sheka da hada kai da masu laifi.

A cikin bidiyon, matashin ya ce wasu daga cikin jami’an suna karɓar kuɗin toshiyar baki daga hannun dillalan ƙwaya da sauran masu aikata laifi, tare da yin biris da laifukan da ake aikatawa a yankin.

Haka kuma, ya bayyana cewa akwai jami’an da ke tsegunta wa masu laifi cewa jami’an tsaro za su kawo samame, wanda hakan ke ba su damar guduwa kafin a kama su.

Matashin ya jaddada cewa irin wannan dabi’a ce ke hana nasarar yaki da laifuka, musamman matsalolin faɗa tsakanin kungiyoyin daba da yaɗuwar shan miyagun ƙwayoyi a cikin birnin Kano.

Sakamakon haka, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan jami’an da ake zargi da hannu a lamarin.

A tsawon lokaci, ana ta samun zarge-zargen cewa wasu jami’an ‘yan sanda na karɓar cin hanci daga hannun masu laifi, musamman masu mu’amala da miyagun ƙwayoyi, don kauce wa gudanar da aikinsu na gaskiya.

Sai dai irin wannan ƙorafi ba kasafai yake kai wa ga matakin bincike ba, lamarin da ke kara rage amincewar jama’a ga rundunar.

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa duk wanda ke da irin wannan ƙorafi zai iya gabatar da shi kai tsaye ga rundunar, tare da tabbacin cewa za a ɗauki mataki ba tare da tsangwama ko barazana ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here