Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Samun Ambaliya a Gurare 76

0
13

Gwamnatin Tarayya ta bayyana hasashen ruwan sama mai yawa da ake sa ran zai ɗauki tsawon kwanaki biyar daga 5 zuwa 9 ga watan Agusta, 2025, wanda zai iya haddasa ambaliya a jihohi 19 da kuma gurare 76 a faɗin ƙasar nan.

Wannan gargaɗi ya fito a ranar Talata daga Cibiyar  Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa (National Flood Early Warning Systems Centre) ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli ta Ƙasa, inda aka bukaci hukumomi da mazauna yankunan da abin zai shafa da su ɗauki matakan gaggawa don kauce wa asara.

Wannan na zuwa bayan ambaliya mai tsanani ta afkawa wasu sassan jihohin Ogun da Gombe a ranar Talata, yayin da wasu jihohin kamar su Legas, Filato, Anambra da Delta suma suka fuskanci irin hakan.

Rahoton hasashen ambaliyar da cibiyar ta fitar ya bayyana cewa ana sa ran ruwan saman zai shafi wurare da dama kamar haka,

Akwa Ibom: Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang

Bauchi: Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a

Ebonyi: Abakaliki, Echara, Ezilo

Cross River: Ogoja Edor, Obubra

Nasarawa: Keana, Keffi, Wamba

Benue: Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya

Kaduna: Jaji, Kafancha, Birnin-Gwari, Zaria

Katsina: Bindawa, Bakori, Daura, Funtua

Kebbi: Bagudo, Birnin-Kebbi, Bunza, Gwandu, Jega, Kalgo, Kamba, Kangiwa, Shanga, Ribah, Sakaba, Saminaka, Yelwa, Gauri-Banza

Kano: Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Birnin Kano, Karaye, Tundun-wada, Wudil, Kunchi

Niger: Kontagora, Rijau, Ringim

Plateau: Mangu

Taraba: Donga, Takum

Jigawa: Diginsa, Gumel, Dutse, Gwaram, Hadejia, Miga

Yobe: Machina, Potiskum

Zamfara: Anka

Sokoto: Sokoto, Wamakko

Borno: Biu

Gombe: Bajoga

Ana shawarci jama’a da su kiyaye, su bi hanyoyin bayar da agajin gaggawa, kuma su kasance cikin shiri domin kare rayuka da dukiyoyin su daga haɗarin ambaliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here