Akalla mutane 22 ne suka rasu, yayin da wasu 20 suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata babbar mota kirar tirela a hanyar Lambata zuwa Lapai a Jihar Neja a Litinin data gabata.
Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC) a Jihar Neja, Aishat Sa’adu, ita ce ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa mutane 42 ne ke cikin tirelar tare da wasu dabbobi lokacin da hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 3 na dare, inda mutane 22 suka mutu a nan take.
Tirelar ta fito ne daga Jihar Kano tana kan hanyarta zuwa Legas kafin ta yi hatsari a tsakanin Lambata da Lapai, tazarar kilomita 10 daga Lambata da kuma kilomita 30 zuwa garin Lapai, hedikwatar ƙaramar hukumar Lapai, inji ta.
A cewar Aishat Sa’adu, an kai gawarwakin mamatan asibitin kwararru na Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin tarayya da ke Lambata domin samun kulawar gaggawa.
FRSC tace gudun wuce Sa’a yayi sanadiyar afkuwar hadarin da kuma yin tafiya a cikin dare.