Kungiyar ‘Yan Asalin Jihar Kano ta Kasa, wato National Forum of Kano Indigenes, ta bukaci Gwamnatin Jihar da ta sake nazari kan yunkurin nadin Saidu Yahya, a matsayin sabon shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta bayyana godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kuma bin tafarkin Kwankwasiyya.
Haka kuma, kungiyar ta jinjinawa Hon. Abba Anas Dala da sauran ‘yan jihar Kano da suka nuna kishin kasa ta hanyar adawa da nadin Barr. Zahraddeen Kofar Mata a matsayin mukaddashin shugaban hukumar a baya.
Sai dai kungiyar ta bayyana damuwarta kan nadin Saidu Yahya, wanda take zargin yana da alaka ta kai tsaye da shugaban Hukumar ICPC na kasa da kuma kasancewa cikin amintattun tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Kungiyar ta bayyana cewa nada Saidu Yahya kan wannan mukami mai muhimmanci na iya zama barazana ga sirrukan gwamnati da kuma iya kawo cikas ga nasarorin da gwamnati ke kokarin cimmawa.