Zamu ci gaba da bada gudunmawa wajen ci gaban ilmin kimiyya – Wali

0
109

Kungiyar tsoffin dalibai kwalejojin kimiyya ta jihar Kano da Jigawa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tallafawa ci gaban su.

Tsohon shugaban kungiyar KASSOSA Alhaji Mustapha Nuhu Wali mni, ne ya sanar da hakan yayin taron cika shekaru goma da KASSOSA Dawakin Kudu aji na 2012 suka yi a karshen makon da ya gabata.

Nuhu Wali wanda kuma mamba ne a kwamitin amintattu na KASSOSA
ya kara da cewa hakan ya zama wajibi duba da irin alfanun da suka samu daga wadannan kwalejojin kimiyya dake jihohin Kano da Jigawa.

“Shakka babu duk matakin da muka taka a rayuwar mu duk ya ta’allaka ne kan horo da muka samu a wadannan kwalejoji, wanda bayan mun gama da shekaru aru-aru akwai sauye da sauye da aka samu wanda suke bukatar shigowar kungiyoyi irin namu don bada tamu gudunmawar.

“Kuma kasancewar addinin musulunci ya kwadaitar wajen yin ayyuka na nagarta da sadakatul jariya, muke kokari don ganin mutum ya shiga cikin ladan, wanda kula da harkar ci gaban ilmi yana ciki.

“Shi yasa lokacin da muka yi shugabanci muka maida hankali wajen ganin mun kyautata tsarin da duk abinda Allah ya bamu, don ‘ya’yan mu su samu ingantaccen ilmin kimiyya kwatancin wanda muka samu”, a cewar Mustapha Nuhu Wali.

Ya kara da cewa zai bada duk gudunmawar da ta kamata wajen gyara gine-gine da suka rushe tare da kyautata harkokin koyo da koyarwa.

Da yake jawabi tun da fari, mataimakin daraktan kwalejin kimiyya ta Dawakin Kudu, Malam Bello Abubakar Bichi, yabawa hobbasan KASSOSA aji na 2012 yayi da tallafin da suka baiwa kwalejin, inda ya bukace su don karfafa zumuncin dake tsakanin su.

“Aji na 2012 sun yi rawar gani matuka kasancewar kokarin su na hada irin wannan taro cikin shekaru 10 bayan sun kammala karatunsu, wanda babban abin jin dadi bai wuce zumuncin da suka rike ba tsawon wadannan shekaru.

“Da haka muke ganin yana kyau takwarorin su, suyi koyi da irin abinda suka yi don taimakawa tsarin”, Bello Abubakar Bichi.

Shi kuwa shugaban riko na kungiyar, Mubarak Sale Bagwai na cewa sun ga dacewar kai taron tsohuwar kwalejin ta su ne don ganin halin da take ciki, tare da sake komawa don ganin irin dimbin gudunmawar da ya kamata su kawo don ci gaban ta.

Kwalejojin kimiyyar dai sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da kwararrun ma’aikatan Gwamnati da suka hadar da Injiniyoyi, Likitoci, sauran kwararru a bangaren kimiyya, ‘yan siyasa da kuma ‘yan kasuwa a ciki da wajen kasar nan.