Rundunar Sojoji ta kama wasu mutane 28 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a cikin harabar Barikin Sojoji da ke Jaji, Jihar Kaduna.
Wadanda aka kama sun haɗa da maza 17 da mata 11, lamarin da ya haifar da fargaba kan yadda amfani da miyagun ƙwayoyi ke ƙara yaduwa tsakanin iyalan sojoji da kuma fararen hula da ke zaune a kusa da barikin.
A cewar Kyaftin Olusegun Abioye, mai magana da yawun Cibiyar Horas da Mayaƙan Ƙasa da ke Jaji, yace an gano mafakar dillalan ƙwayoyin ne a unguwannin Railway da Unguwar Lauya, waɗanda ke cikin harabar barikin.
Ya bayyana cewa an kama akalla mutum 15 da ake zargi da jagorantar safarar ƙwayoyin a yankunan, kuma tuni aka mika su ga Hukumar NDLEA domin cigaba da bincike da daukar mataki.
Kyaftin Abioye ya yi wannan bayani ne a yayin wani rangadi da ya jagoranci manema labarai don ƙaryata jita-jitar cewa sojoji sun rushe wadannan unguwanni.
Ya kara da cewa, duk da cewa wasu unguwanni kamar Unguwar Alasan, Unguwar Alhaji da Unguwar Aboki waɗanda ke cikin harabar barikin na bayar da muhimmiyar gudunmawa ga ayyukan rundunar, amma su ma suna haddasa kalubale da barazana ga tsaro da zaman lafiya.
Kyaftin Abioye ya jaddada cewa kusancin wadannan unguwanni da wuraren atisayen sojoji na iya jefa mazauna cikin haɗari, musamman a lokacin da ake gwajin manyan makamai da kayan yaki.