Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za ta kwashe dukkan fursunonin da ke Gidan Gyaran Hali na Kurmawa, wanda aka gina tun zamanin mulkin mallaka, zuwa sabon gidan yari da aka gina a Janguza, sannan za ta mayar da tsohon gidan kurkukun na Kurmawa gidan tarihi.
Mai bawa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da hakan.
“Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta mayar da dukkan fursunonin da ke Kurmawa zuwa sabon gidan gyaran hali da ke Janguza. Bayan hakan, za a canza Kurmawa zuwa gidan tarihin da zai riƙe kayan tarihi da al’adun Kano,” in ji Adam.
Sabon gidan gyaran halin na Janguza, wanda zai iya ɗaukar fursunoni 3,000, yana cikin muhimman ayyukan sabunta gidajen yari da aka fara a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
An gina Gidan Kurkukun Kurmawa a shekarar 1910 lokacin Turawan mulkin mallaka, kuma an tsara shi don karɓar fursunoni 690. Tun daga lokacin ya zama ɗaya daga cikin fitattun alamomin tarihin zamanin mulkin mallaka da tsarin gyaran hali a Jihar Kano.
A halin yanzu, Kano na da gidajen gyaran hali guda goma. Daga ciki Kurmawa da Goron Dutse suna cikin birnin Kano, yayin da sauran ke yankunan Kananan Hukumomi kamar Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo da Dawakin-Tofa.
Ibrahim Adam ya ce wannan sauyi da za a yi na canza gidan kurkukun zuwa gidan tarihi zai taimaka wajen ilmantarwa da bunkasa yawon buɗe ido a jihar.
“Muna son kare tarihinmu kuma a lokaci guda mu samar da yanayi mafi tsabta da lafiya ga fursunoni,” in ji shi.