Ambaliya da Guguwa Sun Yi Barna a Jahohin Neja da Filato

0
6

Ruwan sama mai ƙarfi tare da guguwa sun yi barna a sassa daban-daban na jahohin Neja da Filato a ranar Lahadi, inda gidaje, gonaki, makarantu da wuraren ibada suka lalace.

A jihar Neja, ambaliya ta mamaye gonaki da dama a yankunan Kafin Koro na karamar hukumar Paikoro da kuma aƙalla ƙauyuka 18 a karamar hukumar Lapai. Cikin ƙauyukan da abin ya shafa akwai Dere, Eshi, Apataku, Tsakanabi, Kuchi Kakanda, Arah, Achiba, Rebba, Ebwa, Pele, Edda, Rigido, Gbami, Yawa, Baka da Muye.

A jihar Filato kuwa, guguwa da ruwan sama sun lalata fiye da gidaje 50 a yankin Shimankar na karamar hukumar Shendam. Hakanan, makarantu biyu na firamare da wani wurin ibada a unguwar Menkaat sun rushe sakamakon lamarin.

Da aka tuntubi Darakta Janar na riko na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Hussaini, ya shaida wa TheCable cewa har yanzu bai samu cikakken rahoto kan abin da ya faru ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here