Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, ya bukaci ‘yan Najeriya da bawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adin mulki na shekaru takwas, kamar yadda suka jure wa mulkin Buhari duk da kura-kuransa.
Da yake magana a talbijin ta Arise News, Aliyu ya ce idan bayan 2031 tsarin Shugaban na yanzu bai amfani ƙasa ba, za a iya canza Tinubu.
Ya kalubalanci jam’iyyun adawa da su fito da ingantaccen tsari, maimakon su yi kira da a kawar da gwamnatin Tinubu.
Ya kuma yi gargadi cewa sauya sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya ka iya janyo rikicin siyasa nan gaba, musamman idan shugaban kasa ya bar jam’iyyarsa bayan wa’adin farko.