Tinubu ya bukaci gwamnoni suyi kokarin ragewa a’lumma talauci

0
14

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci gwamnonin  su mayar da hankali wajen inganta rayuwar jama’a, musamman a yankunan karkara, ta hanyar zuba jari a fannonin lantarki da aikin noma, domin rage matsin rayuwa da fatara.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ake gabatar da sabon shirin gwamnatin tarayya mai taken Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP), wanda Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Ƙasa ya gabatar a taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa.

Shirin RHWDP na da nufin haɓaka tattalin arzikin ƙasa daga tushe ta hanyar tallafa wa mazaɓu 8,809 a jihohi 36 na tarayyar Najeriya, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.

Shugaba Tinubu ya ja hankalin gwamnonin da su yi aiki tare da gwamnati domin sauya halin da al’umma ke ciki a matakin ƙasa da ƙauyuka.

 “Ina roƙonku da mu ƙara azama wajen canza rayuwar jama’armu a karkara. Tattalin arzikimmu yana samun sauƙi, kuma muna kan hanyar farfaɗowa, amma sai mun bai wa yankunan karkara muhimmanci. Muna sane da ƙalubalen da suke fuskanta, don haka mu haɗa hannu mu kawo sauyi,” in ji Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here