Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunan Malam Saidu Yahya zuwa ga majalisar dokoki domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci (PCACC).
Saidu Yahya ya kasance gogaggen jami’i a hukumar ICPC, inda ya rike muƙamai da dama a sashen bincike. Yana da digiri a fannin tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano da kuma na fannin Shari’a. Ya kwashe fiye da shekaru 18 yana gudanar da bincike kan cin hanci, almundahanar kuɗi da karkatar da dukiyar gwamnati.
Haka kuma, Gwamna Abba ya naɗa Barr. Hafsat Ada’u Kutama a matsayin sabuwar Sakatariya da mai ba da shawara ta shari’a ga hukumar, tare da mayar da Barr. Zaharadden Hamisu Kofar Mata zuwa Ma’aikatar Shari’a.
Ya kuma godewa tsohon shugaban hukumar, Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, bisa jajircewarsa da aiki tukuru, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta yi aiki da shi a nan gaba idan bukata ta taso.
Gwamnan ya ce wannan sauyi ya nuna kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yaƙi da rashawa da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a jihar Kano, kamar yadda kakakin gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cikin wata sanarwar daya fitar.