Wasu fasinjoji tara sun rasu, yayin da takwas suka tsira, a wani hatsarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Kwale-kwalen na ɗauke da mutum 17 yawancinsu ‘yan mata ne, lokacin da ya kife yans tsakiyar tafiya daga kauyen Digawa a Jahun LGA zuwa Zangon Maje a Taura, wanda lamarin ya faru tun a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na dare.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta ce jami’anta sun tabbatar da adadin mutanen da suka mutu da kuma waɗanda aka ceto.
NEMA ta sanar da wannan labari cikin wani saƙon data wallafa a safiyar yau Alhamis.