Ma’aikatan jinya da ungozoma sun fara yajin aiki a fadin Najeriya

0
11

Ma’aikatan jinya da ungozoma kimanin 25,000 a karkashin ƙungiyar NANNM sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a yau Laraba, 30 ga Yuli, 2025, a duk faɗin ƙasar nan.

Yajin aikin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwana 15 da suka bai wa Gwamnatin Tarayya, bayan gazawar ta wajen warware matsalolin da suka shafi ƙarancin albashi, rashin alawus, ƙarancin ma’aikata da rashin kayan aiki da suke fuskanta.

Yajin aikin zai shafi asibitocin koyarwa, na ƙwararru, cibiyoyin lafiya na tarayya da na matakin farko a jihohi 36 da Abuja, amma bai shafi asibitocin masu zaman kansu ba.

Ƙungiyar na buƙatar gwamnati ta aiwatar da tsarin aikin ma’aikatan jinya, ƙara alawus, ta ɗauki ma’aikata, da kuma ƙirƙirar sashen kula da ma’aikatan jinya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.

NANNM ta ce yajin aikin ya zama dole saboda gwamnatin tarayya ta gaza yin wani yunkuri na warware matsalolin tun bayan karewar wa’adin da suka bayar a ranar 14 ga Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here