An naɗa sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

0
13

An Nada Zaharaddeen H. Kofar Mata a Matsayin Shugaban Riko na Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci (PCACC) ta Jihar Kano ta sanar da nadin Zaharaddeen H. Kofar Mata, a matsayin Mukaddashin Shugaban Hukumar.

Sanarwar nadin ta fito ne daga wata takarda da ke ɗauke da kwanan wata 28 ga Yuli, 2025, wacce jami’in tsaro na hukumar, L. Dauda, ya sa wa hannu a madadin shugaban hukumar. Wannan nadin ya fara aiki nan take, kuma zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf zai bayar da wata sabuwar umarni akan shugabancin hukumar.

Sanarwar ta ce, bisa kudirin hukumar na tabbatar da dorewar aiki da jagoranci mai inganci, hukumar na sanar da dukkan ma’aikata cewa an nada Zaharaddeen H. Kofar Mata, Esq., a matsayin Mukaddashin Shugaban hukumar daga yau Litinin.

Zuwa yanzu dai babu wani dalili da aka bayyana a hukumance dangane da sauyin shugabancin, sai dai sanarwar ta jaddada cewa nadin zai ci gaba har zuwa wani sabon umarni daga Gwamna Kano.

Kafin wannan nadi, Barrista Muhuyi Magaji Rimingado ne ke rike da kujerar shugaban hukumar tun daga shekarar 2016, bayan da tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje, ya naɗa shi.

Sai dai a watan Yuli na shekarar 2021, aka dakatar da shi, sannan daga baya aka cire shi daga kujerar bayan majalisar dokokin jihar ta ce ta gano wasu kura-kurai a aikinsa.

Amma kotun Ma’aikata ta Ƙasa da ke Kano ta dawo da shi kujerarsa a watan Janairun 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here