Kotu Ta Umarci NYSC Ta Bawa Mata Damar Sanya Siket

0
9

Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umurci Hukumar Kula da masu hidimar ƙasa (NYSC) da ta ba wa ‘yan matan da ke bautar ƙasa damar sanya siket a matsayin kayan sakawa, saɓanin wando.

Kotun ta bayyana cewa takurawar da ake yiwa mata wajen sanya wando yaci karo da ‘yanci, addini da mutuncin ɗan adam da kundin tsarin mulki ya tanada.

A hukuncin da Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta yanke a ranar 13 ga Yuni, 2025, ta bayyana cewa dokar NYSC da ke tilasta sanya wando ga mata kawai ba ta da tushe a tsarin mulki. A ranar Lahadi ne aka bayyana takardar hukuncin bayan tabbatar da sahihancinta.

Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da tsoffin ‘yan bautar ƙasa biyu, Ogunjobi Blessing da Ayuba Vivian, suka shigar, bisa bayyana cewa an tilasta musu sanya wando yayin da suke bautar ƙasa, sannan suka ce hakan ya sabawa addinin Kiristanci da suke bi.

Mai shari’a Yilwa ta yanke hukunci cewa ƙin amincewa da bukatar su na sanya siket ya ci karo da ‘yancin su na bin addinin da suka zaɓa, kuma hakan na iya jefa su cikin tsangwama da ƙasƙantar da mutunci.

Kotun ta kuma umurci NYSC da ta mayar da su cikin jerin masu kammala hidimar ƙasa tare da mika musu takardun shaidar kammala NYSC, waɗanda aka ƙi ba su saboda ƙin sanya wando da suka yi a lokacin bautar ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here