Buhari Ya Ƙi Karɓar Kyautar Jirgin Sama da Agogon Gwal— Garba Shehu

0
15

Mai magana da yawun marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wato Mallam Garba Shehu, ya bayyana yadda tsohon shugaban ya ƙi karɓar wasu manyan kyaututtuka a lokacin da yake mulki, ciki har da jirgin sama da agogon Gwal.

A wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Inside Sources na Channels TV, Garba Shehu ya ce Buhari ya nuna rashin amincewa da karɓar agogon lu’ulu’u da wani ɗan kasuwa a Najeriya ya ƙera da sunan Buhari a jiki. Haka kuma ya ƙi amsar kyautar jirgin sama da gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi masa tayin bayarwa.

“Shehu ya ce: ‘Shugaban ƙasa ya duba agogon ya ce, “Agogon lu’ulu’u? Ba zan iya saka wannan ba. Ku gaya masa mun gode, yana ƙoƙari, amma ku mayar da agogon, ba zan iya amfani da shi ba.”

Haka zalika, ya ƙara da cewa a wata ziyarar da Buhari ya kai birnin Dubai a 2016, sarkin Abu Dhabi ya tambaye shi wane irin jirgi yake so, domin ya bashi a matsayin kyauta.

“Shehu ya ce, ‘Buhari ya amsa da cewa idan gwamnatin Najeriya za a bai wa jirgin, zai karɓa. Amma sarkin ya ce, a’a, kai nake so in bai wa jirgin kai tsaye, har ma bayan ka gama mulki ka ci gaba da amfani da shi.’

“To amma Buhari ya ce, ‘Ba zan karɓa ba. Na gama mulki, ba na buƙatar jirgi, kuma ba zan iya kula da shi ba.’”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here