Kungiyoyin mata sun nemi a basu damar samun kujeru masu yawa a majalisun ƙasa da jihohi

0
16

Gamayyar kungiyoyin mata ta ƙasa ciki da suka haɗar da FIDA, WRAPA, da WACOL, sun gabatar da daftarin dokar da ke neman ƙarin kujeru na musamman ga mata a Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai, da kuma majalisun dokokin jihohi.

Daftarin, wanda aka gabatar wa kwamitin sake nazari akan kundin tsarin mulki na Majalisar Dattawa a Kano, na neman a ware kujeru 37 ga mata a majalisar dattawa, guda ɗaya daga kowace jiha da Abuja. 

Haka kuma, suna neman kujeru 47 a majalisar wakilai da kuma kujeru 3 ga mata a kowace majalisar jiha.

A cewar Dr. Mohamed Mustapha Yahya, wannan yunkuri yana da nufin magance ƙarancin wakilcin mata a siyasa, duba da cewa su ke da kashi 45 zuwa 49 cikin ɗari na masu kada ƙuri’a a lokacin zaɓe.

Habiba Ahmed daga kungiyar WRAPA ta buƙaci gwamnati da ta amince da hakan tare da gyara tsarin zaɓe domin inganta wakilcin mata a harkokin shugabanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here