Hatsarin jirgin ruwa ya hallaka mutane uku a Taraba

0
10

Wani jirgin ruwa ya kife a kusa da tsohuwar gadar Namnai da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku.

Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:20 na dare a ranar Juma’a, lokacin da jirgin ruwan, dauke da fasinjoji da motocci, ya kife a kogin Namnai yayin da yake kokarin ketare hanyar Jalingo-Wukari.

Shugaban masu aikin jigilar ruwa na jihar Taraba, Jidda Mayoreniyo, ya tabbatar da afkuwar lamarin a yayin da yake zantawa da Daily Trust, inda ya ce mutum uku sun rasa rayukansu a hatsarin, yayin da aka ceto wasu da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here