Muna kira ga gwamnati a gaggauta dawo da sunan jami’ar Maiduguri na asali—ASUU

0
14

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU reshen Jami’ar Maiduguri ta yi watsi da matakin Gwamnatin Tarayya na sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University.

A wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar suka fitar bayan taron gaggawa da suka gudanar a ranar 24 ga Yuli, 2025, ASUU ta bayyana cewa wannan mataki cin fuska ne ga ikon gudanar da harkokin jami’o’i, kuma ba a tuntubi jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki ba.

Ƙungiyar ta ce za ta dauki matakin doka don ganin an dawo da tsohon sunan jami’ar, tare da kira ga ASUU reshen ƙasa da sauran al’umma su hana tabbatar da wannan sauyi a matakin dokoki.

ASUU ta jaddada cewa dole ne a kiyaye ikon jami’o’i ba tare da katsalandan na ƴan siyasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here