Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dage aikin tsaftar muhalli da ake gudanarwa a karshen kowane wata, inda ta bayyana cewa ba za a yi aikin tsaftar watan Yuli ba.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun ma’aikatar, Murtala Shehu Umar, cikin wata sanarwa da aka fitar.
A cewar sanarwar, an dage aikin tsaftar ne saboda bikin yaye daliban Jami’ar Northwest da za a gudanar a ranar Asabar, 26 ga, wato Yuli ranar da aka saba gudanar da tsaftar a jihar.
Dakta Hashim ya bayyana cewa duk da dagewar tsaftar, ana sa ran za a ci gaba da gudanar da aikin kamar yadda aka saba a karshen wata mai kamawa.
Ya kuma bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da kula da tsaftar muhallinsu a kowane lokaci, ko da kuwa ba a ba da umarni na musamman ba.