Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, Ya Rasu a Abuja

0
17

Mai martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello, ya rasu yana da shekara 71 a duniya bayan doguwar jinya da yake fama da ita a birnin tarayya Abuja.

Dr. Bello ya zama sarki na 16 a Masarautar Gusau a shekarar 2015, inda ya gaji mahaifinsa. 

Kafin hawansa gadon sarauta, ya yi aiki a ma’aikatar gwamnati inda ya rike mukamai daban-daban, har ya kai matsayin Babban Sakatare a tsohuwar Jihar Sakkwato.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhininsa game da rasuwar sarkin, yana mai cewa wannan babban rashi ne da ya shafi kowa da kowa a jihar.

 Kakakinsa, Sulaiman Idris, ne ya isar da sakon ta’aziyyar gwamnati ga iyalan Gusau da daukacin al’ummar jihar.

Gwamna Lawal ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai imani da gaskiya, wanda ya yi wa jama’arsa hidima da sadaukarwa da amana. Ya yi addu’ar Allah ya ji kansa, ya kuma bai wa iyalansa da mabiyansa hakuri da juriya.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here