Yilwatda na shirin zama sabon shugaban APC na ƙasa–Jaridar The Sun

0
15

Rahotanni daga jaridar The Sun sun bayyana cewa tsohon kwamishinan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) kuma Ministan Harkokin Jinƙai na yanzu, Injiniya Nentawe Goshwe Yilwatda, na daga cikin manyan ’yan takara da ake ganin zai iya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Ko da yake ba a sanar da sunansa a hukumance ba, rahotanni na nuna cewa zaɓin nasa ya biyo bayan tattaunawar sirri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayig wamnonin APC a wani taron sirri a fadar shugaban ƙasa da yammacin ranar Laraba.

Idan har aka tabbatar da zaɓinsa, hakan zai kawo ƙarshen jita-jita da cece-kuce na makonni da dama dangane da wanda zai gaji Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ajiye mukamin shugaban jam’iyyar saboda dalilan lafiya.

Wani mamba na kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar (NWC), wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa jaridar cewa jam’iyyar na fatan samun shugaba mai fahimtar dimokuraɗiyya da nagartar shugabanci, ba tare da dogaro da tsoffin ɗan siyasa ba. Haka kuma, zaɓin Yilwatda na da alaƙa da yunƙurin samar da daidaito tsakanin mabiya addinai a shugabancin jam’iyyar.

Yilwatda ya tsaya takarar gwamnan jihar Filato a zaɓen 2023 ƙarƙashin APC, sannan yanzu haka yana rike da mukamin Ministan Harkokin Jinƙai. A baya kuma ya kasance Kwamishinan Zaɓe na INEC a Jihar Benue tun bayan nadinsa a shekarar 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here