Adamu Garba: APC da Gwamnatin Tinubu Na Fuskantar Barazana a Zaɓen 2027

0
19

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Adamu Garba, ya ce jam’iyyar su da gwamnatin Shugaba Tinubu na fuskantar babban kalubale a zaɓen 2027, musamman daga Arewa.

A cewarsa, rashin Buhari ya bar gibi a cikin jam’iyyar, kasancewar shi ne ya jawo ƙuri’un da suka bai wa APC nasara a 2015 da 2019. Ya ce idan ba a sake tsarin jam’iyyar da haɗa masu ruwa da tsaki ba, za a fuskanci rashin nasara.

Ya kuma bayyana cewa yawancin magoya bayan Buhari na sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC, lamarin da ke barazana ga APC.

Adamu Garba ya soki yadda wasu shugabannin jam’iyyar ke ƙin fadin gaskiyar halin da ake ciki, yana mai cewa tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki na kara jefa talakawa cikin damuwa, musamman a arewacin Najeriya.

Ya bukaci a nemo shugaba nagari da kowa ya yarda da shi, domin gyara tafiyar APC kafin lokaci ya kure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here