Sanata Sampson Ekong mai wakiltar Akwa Ibom ta Kudu da Aniekan Bassey, dan majalisar daga Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas, sun sanar da sauya shekar su daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikun sauya shekar yayin zaman majalisar da aka gudanar a ranar Laraba.
A cikin wasikarsa, Aniekan Bassey ya bayyana cewa ya yi dogon tunani kafin yanke wannan hukuncin, wanda ya ce ya samo asali ne daga halin da ake ciki a siyasar mazabarsa da kuma matsalolin cikin jam’iyyar PDP da suka gagara gyarawa.
Shi ma a nasa bangaren, Sanata Sampson Ekong ya bayyana cewa sauya shekar tasa ta biyo bayan tattaunawa mai zurfi da kuma shiga jam’iyyar APC da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya yi.