Hisbah ta sanar da lokacin ɗaurin auren yaran da suka taɓa ɗaurawa kansu aure a Kano

0
21

Rundunar Hisbah ta jihar Kano, reshen ƙaramar hukumar birni ta sanya Jumaʼa 1 ga Ogusta, a matsayin ranar daura auren matasan da suka taɓa ɗaurawa kansu aure ba tare da sanin iyaye ba, wato Aliyu da Fatima, dukkan su mazauna unguwar Yakasai dake ƙwaryar birnin Kano.

Shugaban Hisbah, na karamar hukumar birnin Kano Hamidan Tanko Alasaka, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, yana mai cewa an cimma matsaya tsakanin iyayen yaran da Hisbah, akan cewa za’a daura wannan sabon aure a ofishin Hisbah ta karamar hukumar birni a ranar 1 ga watan Ogusta na wannan shekara.

Akan haka ne hukumar ke neman al’umma su tallafawa masu niyyar yin auren, musamman waɗanda suka yi alkawarin bayar da tallafin tun da farko. Yace akwai mutanen da suka yi alkawarin bayar da tallafi ga masu shirin zama ango da amarya amma kawo wannan lokaci tallafin bai zo hannun Hisbah ba.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne, matasan suka ɗaurawa kansu aure ba tare da sanin iyayen su ba, saboda tsananin kaunar da suke yiwa juna, wanda hakan ne yasa iyayen Fatima garzayawa ofishin Hisbah da manufar a kashe auren, saboda bai cika sharudan addinin Islama ba.

Haka ne yasa rundunar Hisbah ta karamar hukumar birnin Kano ayyana auren a matsayin wanda baya kan ƙa’ida tare da rushe shi, duk da cewa daga baya iyayen yaran sun amince azo ayi sabon aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here