Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Akwa Ibom, CP Baba Mohammed Azare fsi, ya mika takardun biyan kuɗi na naira miliyan talatin da bakwai da dubu dari biyu da tamanin da dari biyu da casa’in da shida da kobo talatin da shida (N37,280,296.36k) ga iyalan jami’an da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikinsu.
Wannan tallafi na cikin shirin jin ƙai da inshorar rayuwa da shugaban ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Olukayode Egbetokun, PhD, NPM, ya kafa, inda aka mika kuɗin ga mutum talatin da uku (33) da suka kasance ‘yan uwa na kusa ga jami’an da suka mutu.

Yayin mika takardun, CP Baba Mohammed Azare fsi ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƴan sandan ƙasa bisa wannan karamci, yana mai cewa kuɗin za su taimaka matuƙa ga iyalan, kuma hakan alama ce da ke nuna cewa sadaukarwar da jami’an suka yi bata tashi a banza ba.
Kwamishinan ya jaddada cewa shugaban ƴan sandan ƙasa yana da damuwa matuƙa kan walwalar jami’ai da ma’aikatan rundunar ‘yan sanda. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba za ta daina gudanar da irin waɗannan shirye-shirye na tallafi ba, musamman ga iyalan waɗanda suka sadaukar da rayukansu domin zaman lafiya da cigaban ƙasa.