Gwamnatin Kano zata ɗaga darajar asibitin Daɓai

0
11

A kokarinta na inganta fannin kiwon lafiya da tabbatar da kulawa ta inganci ga al’umma, Gwamnatin Jihar Kano ta dauki sabon mataki na bunkasa ayyukan asibitocin jihar. Wannan ya biyo bayan ziyara bazata da Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya kai asibitin Daɓai da ke karamar hukumar Dala.

A yayin ziyarar, Kwamishinan ya bayyana cewa daga yanzu asibitin zai ci gaba da aiki na tsawon awanni 24 a rana, sabanin tsarin awanni 12 da ake amfani da shi a baya. 

Ya ce wannan matakin ya biyo bayan karuwar bukatar jama’a na samun kulawa da agajin gaggawa a kowane lokaci.

Dr. Yusuf ya kuma bayyana cewa nan ba da jimawa ba, gwamnati za ta daukaka matsayin asibitin daga na kula da lafiya a matakin farko zuwa babban asibit, duba da yawan jama’ar da ke cin gajiyarsa. 

Ya bayyana cewa asibitin na hidimtawa al’umma daga kananan hukumomin Dala, Ungogo da Gwale.

Bayan zagayen da ya yi a sassa daban-daban na asibitin, Kwamishinan ya yaba da ƙwazon ma’aikatan asibitin duk da wasu ƙalubale da ake fuskanta, musamman a bangaren kayan aiki da sassan da ke bukatar gyara.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta gyara asibitin da ƙara masa yawan ma’aikata, tare da mayar da ma’aikatan wucin gadi zuwa ma’aikatan dindindin domin karfafa musu guiwa da inganta ayyukan kiwon lafiya a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here