An Ɗage Sauraron Ƙarar Zargin Karkatar da Kuɗi a Hukumar Zaɓe ta Kano

0
10

Babbar Kotun Tarayya mai lamba shida da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Da Dangogin su ta ƙasa (ICPC) ta shigar, kan zargin karkatar da kuɗi a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, lokacin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a shekarar 2024.

ICPC na zargin Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, tare da wasu ma’aikata biyu, da karkatar da naira biliyan ɗaya da dubu ɗari biyu, waɗanda ake cewa an kashe su ba bisa ƙa’ida ba.

A zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin, 21 ga Yuli 2025, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a J.J. Malik, Kwamishinan Hukumar Zaɓen Kano, Barr. Muktar Garba Ɗandago, ya bayyana cewa an fara sauraron shari’ar, amma kotun ta dakata da cigaba da sauraron ƙarar saboda rashin halartar wadanda ake tuhuma.

Lauyan ICPC, Barr. Enosa Omoghibo, wanda shi ne mataimakin darakta a sashen shari’a na hukumar, ya bayyana wa kotu cewa ba a ga waɗanda ake tuhuma ba a zaman, lamarin da ya hana cigaba da shari’ar.

Sai dai lauyan da ke kare shugaban hukumar, Barr. Mahmud Magaji (SAN), ya shaida wa kotu cewa ba a mika sammaci ga waɗanda ake ƙara ba kamar yadda doka ta tanada, wanda hakan ya hana su halartar zaman.

A cewar Barr. Ɗandago, mai shari’a J.J. Malik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga Nuwamba, 2025 domin ba da damar gayyatar waɗanda ake ƙara ta hanyar da doka ta gindaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here