Babbar kotun tarayyar karkashin jagorancin alkali Simon Amobeda, ce ta Kori karar wadda Jam’iyyar APC da shugaban ta na jihar Kano Abdullahi Abbas, da Hon Aminu Aliyu Tiga, suka shigar suna neman hana biyan kudaden kananan hukumomin daga asusun gwamnatin tarayya.
Tun da farko APC ta shigar da ƙarar akan neman kotu ta bayar da umarnin hana gudanar da zaɓen ƙananun hukumomin Kano, sai dai bayan da aka yi zaben, suka koma neman hana turowa ƙananun hukumomin kuɗi tunda an bijirewa umarnin kotu wajen yin zaɓen.
Lauyan masu kara Barista Sunday Olowomoran, shine ya nemi kotu ta jingine karar amma hakan bai samu ba.
Lauyan gwamnatin jihar Kano, da ƙananun hukumomi, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi, kuwa ya nemi APC ta biya su kudin bata musu lokaci har Naira biliyan 2, bayan da mai shari’a Amobeda, yayi watsi da ƙarar.