Kwamitin PTA a Kano ya nuna damuwa akan kisan ɗalibai a Sakandiren Bichi

0
18

 

Shugaban kwamitin haɗin gwiwa na malamai da iyayen ɗaliban makarantun Firamare (PTA) a jihar Kano, Malam Salisu Abdullahi, ya bayyana matuƙar damuwa da takaicinsa kan kisan wasu dalibai guda biyu da aka ce abokan karatunsu ne suka yi a wata makarantar sakandare da ke garin Bichi.

Yayin ganawa da manema labarai, Malam Salisu ya ce lamarin ya faru ne sakamakon gazawar iyaye wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu bisa koyarwar addinin Musulunci.

A cewar sa wannan abin da ya faru yana da alaka da rashin kulawa daga iyaye. Iyaye na da nauyin bawa ’ya’yansu tarbiyya mai kyau domin kauce wa irin wannan mummunan lamari.

Ya ce kwamitin PTA na jihar zai bi diddigin wannan al’amari tare da ɗaukar tsauraran matakai domin hana faruwar irin hakan a nan gaba.

Haka kuma, Malam Salisu ya yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wani dalibi da aka ga yana nuna halayen rashin ɗa’a ko ɗabi’un tashin hankali, domin a ɗauki matakin gaggawa kafin abin ya kai ga haifar da barazana.

Ya kuma nuna godiya ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bayarwa ga kwamitin a koda yaushe. Haka nan ya yaba da jajircewar rundunar ’yan sandan jihar wajen tabbatar da tsaro a makarantu da fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here