Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta yi barazanar shiga yajin aiki a fadin ƙasar nan idan gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatun su kafin ranar 23 ga Yuli, lokacin da wa’adin kwanaki 21.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Bala Audu, ya ce sabon tsarin alawus da gwamnati ta fitar bai yi daidai da yarjejeniyar da aka cimma a baya ba, kuma yana tauye walwalar likitoci.
Ya ce NMA na ci gaba da tattaunawa da gwamnati, inda suka gana da Ministocin Lafiya, amma taron na baya-bayan nan bai gudana ba saboda rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Farfesa Audu ya jaddada cewa idan ba a warware matsalolin cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ba, babu makawa sai likitoci suka dakatar da aiki a faɗin Najeriya.