Duk da cewa tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya fito daga Daura a Jihar Katsina, ana ci gaba da nuna masa girmamawa a Jihar Borno, musamman a birnin Maiduguri, inda gine-ginen gwamnati da dama ke ɗauke da sunansa.
Wannan rahoto na bayani ne game da muhimman wurare biyar a Maiduguri da aka sanya wa sunan Buhari, a matsayin girmamawa da kuma nuna tasirin mulkinsa da kyakkyawar alakar da yan jihar ke nuna masa.
Ga wasu jerin gurare 5 da aka sanyawa sunan Buhari a Maiduguri;
1. Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa, na Muhammadu Buhari, a Maiduguri.
Tsohon sunan wannan filin jirgin saman shi ne Maiduguri Airport, sai dai a shekarar 2023 gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta sauya sunansa zuwa General Muhammadu Buhari International Airport. Hakan ya kasance cikin wata takarda da Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta fitar a ranar 1 ga Yuni, 2023, inda aka bayyana cewa an sauya sunayen filayen jirage 15 domin karrama fitattun ‘yan Najeriya.
2. Cibiyar Kula da masu damuwa ta Muhammadu Buhari, Maiduguri
Wannan cibiyar kula da masu fama da rauni da damuwa tana ɗaya daga cikin wuraren da aka gina domin tallafa wa al’umma musamman a yankin Arewa maso Gabas.
3. Makarantar Muhammadu Buhari Academy, Maiduguri
An ƙaddamar da wannan makaranta ta kwana a shekarar 2019. An gina ta ne a kan hanyar Baga domin kula da yaran da yaƙin Boko Haram ya mayar dasu marayu. Makarantar tana ba da horo da tarbiyya ga waɗanda suka rasa iyayensu sakamakon rikicin ta’addanci.
4. Ginin Majalisar Jami’ar Maiduguri (Senate Building)
Ginin da TETFund ta gina kuma aka ƙaddamar a ranar Litinin, 16 ga Yuli, 2018, an sanya masa sunan Muhammadu Buhari. Wannan gini yana kusa da shingen shiga jami’ar kuma ana iya ganinsa daga titin da ke waje.
5. Jami’ar Muhammadu Buhari, Maiduguri
A ranar 17 ga Yuli, 2025, a wani zama na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa za a sauya sunan University of Maiduguri zuwa Muhammadu Buhari University. A cewar Tinubu, wannan yunkuri wani bangare ne na girmamawa ga tsohon shugaban ƙasa Buhari bisa gudummawar da ya bayar ga ƙasa.