A wasu makarantu a ƙaramar hukumar Takai ta Jihar Kano, irin su Karfi Primary School da Shawu Islamiyya Primary School, ɗalibai na karatu a cikin mawuyacin hali.
Binciken dandalin MonITNG ya gano cewa yara suna cunkushe a ɗakunan karatu masu laka, ma’ana ba siminti ba, ba tare da kujeru, tebura, allo ko kayan koyarwa ba.
Rufin ajujuwan na na cikin mawuyacin hali, kuma dalibai kan zauna a ƙasa mai ƙura da sauran yanayi mara kyau ga lafiyar ɗan adam.

A Karfi, dalibai kan fuskanci zubar ruwa akan su a lokacin damina, lamarin da ke hana ci gaba da darasi.
Rahoton asusun tallafawa ƙananun yara na Majalisar ɗinkin duniya UNICEF ya nuna cewa Kano na da fiye da yara 989,000 da ba sa zuwa makaranta. Inda a Karfi kaɗai, yara fiye da 10,000 ke karatu ba tare da makarantun zamani ba.

Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin jihar Kano, ta bakin gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta ɓaci akan lalacewar al’amuran karatu da manufar inganta fannin, sai dai har yanzu akwai guraren ɗaukar karatu dake bukatar ɗaukin gaggawa.