ADC Ta Soki Tinubu Akan Bawa Yan Arewa Mukamai

0
6

Jam’iyyar ADC ta soki sabbin nadin mukamai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, tana mai cewa yunkuri ne na ƙoƙarin na nuna cewa yana tare da yan arewa bayan fiye da shekara guda na watsi da yankin.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce Tinubu ya makara wajen yin nadin, domin ba za a manta da irin wariyar da yankin Arewa ya fuskanta a cikin mulkinsa ba.

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin Tinubu da mantawa da Arewa a lokacin da ‘yan bindiga ke addabar kauyuka, manoma na barin gonaki, da talauci ke ƙara ta’azzara bayan cire tallafin fetur ba tare da tsari ba.

ADC ta ce nadin mukaman yanzu ba komai ba ne illa yunkurin rarrashi saboda fargabar adawa mai ƙarfi daga Arewa, tana mai kira ga gwamnati da ta daina siyasar rarrashi tare da rungumar gaskiya da adalci ga kowa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here