Shugaban EFCC: Gwamnoni 18 da ke kan mulki na fuskantar bincike

0
7
Ola Olukoyede

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ana binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki a halin yanzu bisa zargin aikata laifukan cin hanci da rashawa.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Legas yayin wani taron wayar da kai game da illolin lalatawa da kuma cin zarafin takardun kudi na Naira.

A cewarsa, hukumar za ta ɗauki matakin shari’a da zarar wa’adin mulkin waɗanda ake binciken ya ƙare.

Shugaban EFCC ɗin ya bada misalin yadda wani tsohon gwamna ya tsere zuwa ƙasar Ingila, kwana guda bayan mika mulki, domin guje wa kama shi da EFCC za ta yi. Ya bayyana cewa an taba kama gwamnan yana watsa kuɗin fam a wani otel a Ingila.

Olukoyede ya ce akwai wani lokaci suna yin binciken wani gwamna a lokacin yana kan mulki. Ba sai sun gama mulki ba muna fara bincike. Yanzu haka, muna binciken gwamnonin da suka kai 18 da ke kan mulki. Da zarar sun sauka, za mu ci gaba da É—aukar mataki gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here