Malamin Jami’a Ya Rasu Bayan Lalata da Ɗalibar sa a Otel

0
23

Wani malami a Jami’ar Prince Abubakar Audu da ke Ayingba, Jihar Kogi, mai suna Olajide Abimbola Ibikinle, ya rasu bayan da ya sadu da wata ɗaliba a ɗakin otel.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar malamin, wanda ke koyar da darussan Ilimin Kimiyyar Halayyar Ɗan Adam, a wani otel da ke Ayingba, jim kaɗan bayan ya kammala saduwa da ɗalibar sashen da yake koyarwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa ɗalibar da ake magana a kai, mai suna Glory Ojochegbe Samuel, ita ce ta sanar da ma’aikatan otel ɗin haka bayan da ta lura cewa malamin ya daina motsi bayan sun kammala saduwar.

An garzaya da shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Aya, ya ce tuni rundunar ta tsare ɗalibar tare da mayar da ita zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Lokoja domin ci gaba da bincike. Ya ƙara da cewa rundunar na gudanar da bincike sosai kan lamarin, kuma za a ɗauki matakin da ya dace bayan kammala bincike.

A nata ɓangaren, hukumar gudanarwar jami’ar Prince Abubakar Audu ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana shi a matsayin wani abin takaici da ya ɗauki hankalin al’umma.

Cikin wata sanarwa da maga takardan jami’ar, Barista Yahaya Segun Aliu, ya fitar, jami’ar ta jajanta wa iyalan marigayin, tare da bayyana damuwa game da yadda lamarin ya wakana.

Sanarwar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun shiga bincike domin gano musabbabin rasuwar malamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here