Daya daga cikin manyan asibitocin masu zaman kansu a Birtaniya, London Clinic, ya shiga cikin abubuwa masu ɗaukar hankalin jama’a bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a cikin asibitin ranar Lahadi da ta gabata, 13 ga Yuli, 2025.
Buhari da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, dukkansu sun kwanta a wannan asibiti. Yayin da Abdulsalami ya samu sauƙi kuma aka sallame shi, Buhari ya rasu a ranar Lahadi, duk da cewa an ce yana cikin nishaɗi a ranar Asabar 12 ga Yuli, kuma yana shirin samun sallama daga asibitin.
Mamman Daura, ɗan uwan marigayin, ya bayyana cewa Buhari yana cikin yanayin murmurewa da annashuwa a ranar Asabar kafin lafiyarsa ta sake ɗaukar sauyi a tsakiyar ranar Lahadi.
Buhari dai ya tafi Birtaniya a watan Afrilu domin duba lafiyar da ake yi masa a kai a kai, amma daga bisani ya kamu da sabuwar rashin lafiya a can.
Ko da yake ba a bayyana rashin lafiyar da tayi sanadiyar mutuwar sa ba, sai dai an tabbatar da cewa Buhari ya shafe shekaru da dama yana fama da rashin lafiya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa ya kwashe wani lokaci a sashen bayar da kulawa ta musamman (ICU) a cikin asibitin London Clinic.
An kafa The London Clinic tun a shekarar 1932, kuma yana daga cikin manyan asibitoci masu zaman kansu a Birtaniya. Asibitin ya shahara wajen kula da marasa lafiya masu cutar daji (cancer), cututtukan ciki, ciwon ƙashi da jijiyoyi, da kuma tiyatar ƙawata jiki.
Asibitin ya yi wa dubban marasa lafiya daga sassa daban-daban na duniya magani, ciki har da shugabanni na siyasa da kuma wasu daga cikin dangin gidan masarautar Birtaniya.
Wani likitan Najeriya da ke aiki a Birtaniya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Saturday PUNCH cewa asibitin na da ingantattun kayan aiki, manyan kwararru da kuma abokan huldar da suka fito daga manyan gurare a duniya.
Ya ce farashin ganin likita a asibitin ya tashi daga fam 100 zuwa fam 750, gwargwadon nau’in matsalar mara lafiya.
Likitan ya ƙara da cewa ya san wasu likitoci ‘yan Najeriya guda biyu da suka taba aiki a wannan asibiti, kuma ya bayyana cewa farashin CT Scan a nan na iya kaiwa kusan fam 500, yayin da manyan tiyata ke kaiwa daga fam 10,000 zuwa fam 13,000.
Game da masauki kuwa, ya bayyana cewa akwai matakai daban-daban, ɗakin kwana na gama gari yana kaiwa daga fam 1,000 zuwa fam 1,800 a kowane dare, ɗakin VIP ko na alfarma yana tsakanin fam 1,800 zuwa fam 2,500, yayin da kwana a sashen kulawa ta musamman (ICU) ke kaiwa tsakanin fam 3,000 zuwa fam 3,500 a dare daya