Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kusa da kauyen Jangebe da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara, inda suka kashe manoma tara sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 15 a ranar Juma’a.
Shaidu daga yankin sun bayyana cewa maharan, dauke da bindigu a kan babura, sun kewaye manoman da ke aikin gona tare da bude musu wuta, lamarin da ya janyo asarar rayukan mutane da dama. Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa maharan sun dade suna zagaye gonakin kafin su kai harin.
Yahaya Yari Abubakar, wani jigo a harkar siyasa daga yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “’Yan bindiga sun kai hari kan manoma, sun kashe tara daga cikinsu.”
Rahotanni sun ce daga cikin waɗanda aka kashe har da shugaban sa-kai na kauyen Jangebe tare da abokan aikinsa guda biyar, da kuma wasu mazauna kauyen guda uku. Har yanzu ba a samu labarin waɗanda aka yi garkuwa da su ba.