Najeriya tayi gwajin Jiragen sama marasa matuki da aka kera a cikin gida

0
10

Cibiyar Koyar da Harkokin Sufuri ta ƙasa (NITT) da ke Zariya, jihar Kaduna, ta kaddamar da gwajin farko na jirage sama marasa matuki da injiniyoyinta na cikin gida suka ƙera.

An gudanar da gwajin ne a hedkwatar cibiyar da ke Zariya a ranar Juma’a, al’amarin da ke nuna ci gaba da jajircewar cibiyar wajen kirkire-kirkire da inganta fasahar sufuri a Najeriya.

Shugaban cibiyar, Farfesa Bayero Salih Farah, wanda ya halarci gwajin, ya bayyana jin daɗinsa da gamsuwa bisa yadda aka ƙera jiragen. Ya bayyana jiragen a matsayin wata alama ta ci gaba da nasarar da NITT ke samu a fannin ƙirƙire-ƙirƙire da ƙarfafa fasahar sufuri cikin gida.

“Ina ganin wannan a matsayin wani muhimmin mataki na farko. Muna fatan ganin ranar da irin waɗannan jiragen za su fara taka rawa a harkokin sufuri a ƙasarmu,” in ji Farah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here