Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta tabbatar da kama dalibai 11 na makarantar sakandare ta kwana da ke Bichi bisa zargin hannu a kisan gilla da aka yi wa wasu abokan karatunsu biyu.
An bayyana sunayen waɗanda aka kashe da Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa, waɗanda ake zargin cewa abokan karatunsu ne suka kai musu hari da wasu ƙarafa masu kaifi da ake kira “Gwale-Gwale”.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama daliban 11 da ake zargi, kuma tuni an fara gudanar da bincike domin gano irin rawar da kowane ɗalibi ya taka a cikin lamarin.
“Rundunar ta himmatu wajen tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu,” in ji Kiyawa
Za a ci gaba da gudanar da bincike don gano cikakken bayani game da wannan mummunan al’amari.