Wani masoyin tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, Alhaji Sirajo Yazid-Abukur, ya bada tallafin Naira miliyan ɗaya ga ma’aikatan da suka haƙa kabarin da aka binne Buhari a gidansa da ke Daura.
Alhaji Yazid-Abukur, wanda shi ne Manajan Darakta na Hukumar Gyara hanyoyi ta jihar Katsina (KASSROMA), ya bayyana hakan ne a Katsina ranar Alhamis, biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka nuna ma’aikatan suna haƙa kabarin.
A cewarsa, shugaban tawagar masu haƙa kabarin, Muhammad Ali, zai karɓi Naira dubu 500,000, yayin da sauran biyu za su karɓi Naira 250,000 kowannensu.
Ya bayyana cewa ya riga ya aika a nemo mutanen, domin a cewarsa, kudin na iya zama jari da za su iya fara wani kasuwanci da zai tallafa musu da iyalansu.
Alhaji Yazid-Abukur, ya kuma yaba da irin jajircewar da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya nuna tun kafin jana’iza, lokacin jana’iza da bayan haka.
Ya ce halartar gwamnan da kansa wajen binne marigayin alama ce ta biyayya, tawali’u da kuma cancanta a matsayin shugaba.
Shugaban na KASSROMA ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayi Buhari, tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.