Al’ummar Musulmi na gudanar da bikin ranar Mauludi a sassan Duniya

0
119

Yau Al’ummar Musulmin duniya ke gudanar da bukukuwan ranar Maulid el Nabiyy, ko kuma tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) kamar yadda aka saba yi kowacce ranar 12 ga watan Rabiu Awwal a kalandar Islama.

Bisa yadda aka saba, akan shirya tarurruka inda malaman addinin Islama ke gabatar da kasidu akan tarihin Manzon Allah (SAW) domin fadakar da jama’a irin kyawawan halayen fiyayyen halitta da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen gabatar da sakon manzancin da Allah ya aiko shi ga duniya.

Yayin gudanar da irin wadannan tarurruka, daliban makarantu kan rera baitukan yabo ga fiyayyen halittar, Annabi Muhammad (SAW) domin karrama shi da kuma fadakar da matasa akan irin gudummawar da ya bayar wajen isar da sakon annabta da kuma muhimmancin karrama shi tare da nuna kauna ga iyalan gidansa.

A kowacce shekara kasashen Musulmi da dama kan bada hutu a irin wannan rana domin gudanar da irin wadannan bukukuwan Mauludi a birane da kauyuka.

Gwamnatin Najeriya ta ware ranar litinin mai zuwa a matsayin ranar hutu domin bada damar gudanar da bukukuwan Maulidin a hukumance, yayin da yanzu haka aka fara gudanar da bukukuwan a garuruwa da dama.

Wasu jama’a kan yi amfani da watan Rabiu Awwal baki daya wajen gudanar da bikin Maulidin a garuruwa daban daban.