Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya rage farashin litar man fetur zuwa Naira 895 a Abuja da Naira 865 a Legas.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa a yau Laraba gidajen mai na NNPC a Abuja na sayar da man fetur kan Naira 895 akan kowacce lita saɓanin tsohon farashin Naira 910.
Haka zalika, a Legas, NNPC sun rage farashin man fetur zuwa Naira 865 a lita bisa rashin Naira20 daga tsohon farashin Naira 885.
Wannan sauyin farashi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar gasa a harkar sayar da mai tsakanin NNPC da matatar man Dangote.
A ranar 8 ga Yuli, Matatar Man Dangote da ke Legas ta saukar da farashin litar mai a matakin zuwa Naira 820, mako guda bayan ta rage daga Naira 940 zuwa Naira 840.
Don magance damuwa game da hauhawar farashin man fetur da matsalolin wadatar sa, gwamnatin tarayya ta tsara gudanar da taron masu ruwa da tsaki a fannin mai a ranakun 23 da 24 ga Yuli.