Buhari yayi bakin kokarin sa akan gyara Najeriya—Obasanjo

0
13

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi, ba ga iyalinsa kaɗai ba, har da Najeriya baki ɗaya.

Obasanjo ya ce kwarewar dukkan waɗanda suka taɓa jagorantar ƙasar na da matuƙar muhimmanci wajen fitar da Najeriya daga mawuyacin halin da take ciki.

Ya ƙara da cewa Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa wajen hidimtawa ƙasa don gyara ta, tare da roƙon Allah ya yafe masa kura-kurensa, ya kuma bashi  Aljannah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here