Abubuwan da ya kamata ku sani akan rayuwar marigayi tsohon shugaban ƙasa Buhari

0
21

An haifi Muhammadu Buhari a watan Disamba, 1942 a Daura, Jihar Katsina. Mahaifinsa Bafulatani ne, ya rasu tun Buhari na ƙarami, inda ya tashi a hannun mahaifiyarsa ‘yar kabilar Kanuri. A cewarsa, shi ne na 23 a cikin ‘ya’yan mahaifinsa, kuma na 13 daga wajen mahaifiyarsa.

Buhari ya fara fitowa fili a shekarar 1983 lokacin da ya jagoranci rundunar sojin Najeriya wajen korar sojojin Chadi daga wasu tsibirai na tafkin Chadi. Daga baya sojoji suka kifar da gwamnatin Shehu Shagari, inda Buhari ya hau mulki a matsayin shugaban soja, duk da cewa ya ce ba shi ne ya jagoranci juyin mulkin ba.

Mulkinsa ya ɗauki watanni 20 kacal kafin wani juyin mulki ya kifar da shi. A lokacin mulkinsa na soja, an fi tunawa da yaƙin da ya yi da rashin ɗa’a da cin hanci, inda aka tsare ‘yan siyasa da dama a lokacin.

Bayan mulkinsa, ya koma rayuwa mai sauƙi har sai da janar Sani Abacha ya naɗa shi shugaban Asusun Rarar Man Fetur (PTF), wanda ya samar da ayyuka da dama na ci gaban ƙasa.

A siyasance, Buhari ya fara takarar shugaban ƙasa a 2003, sannan ya sake takara a 2007 da 2011, amma ya sha kaye a dukkan lokutan. Bayan haka, ya ce ba zai sake tsayawa takara ba. Amma canjin yanayi a siyasar Najeriya da rashin jin daɗin al’umma da gwamnatin Goodluck Jonathan ya dawo da shi cikin fafutukar neman mulki a 2015.

A zaben shekarar 2015, Buhari ya lashe zaɓe kuma ya zama shugaban ƙasa na farko daga jam’iyyar adawa da ya kayar da shugaban da ke kan mulki a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya. Ya samu nasarar lashe wa’adi na biyu a 2019.

Daya daga cikin manyan ƙalubale da ya fuskanta a mulkinsa shi ne rashin lafiya. Ya kwashe watanni yana jinya a Landan, lamarin da ya shafi aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsarensa.

Daga karshe ya rasu a Landan a ranar Lahadi 13 ga watan Yuli na shekarar 2025, bayan doguwar jinya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here