Tinubu ya sanar da mutuwar tsohon shugaban ƙasa Buhari

0
86

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Ya Kuma Umarci Mataimakinsa Ya Tafi Ƙasar Ingila Don Dawowa Da Gawarsa.

Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Na Musamman Kan Harkokin Bayani Da Tsare-Tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a yau Lahadi.

A cewar sanarwar, Buhari ya rasu ne a birnin London da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau, bayan fama da doguwar jinya.

Shugaba Tinubu ya ya tuntubi uwargidar marigayin, Hajiya Aisha Buhari, inda ya miƙa ta’aziyyarsa da jajantawa ga iyalansa da al’ummar Najeriya baki ɗaya.

A matsayin ɗaya daga cikin matakan girmamawa, Shugaba Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ya tafi ƙasar Birtaniya domin rakiyar gawar Buhari zuwa gida Najeriya.

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya shugabanci ƙasar a matsayin zababben shugaban ƙasa sau biyu a shekarar 2015 da kuma 2023.

 Haka kuma ya rike matsayin shugaban mulkin soja daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a sauke tutocin Najeriya zuwa rabin sanda a fadin ƙasa, domin nuna alhini da girmamawa ga marigayi shugaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here