Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya bayyana cewa yana duba yiwuwar sayar da matatun man fetur na gwamnati zuwa ga yan kasuwa.
Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ne ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi da Bloomberg, inda ya ce ana sake nazari kan tsarin gudanar da matatun, tare da fatan kammala wannan bincike kafin ƙarshen shekarar 2025.
A cewar Ojulari, gyaran matatun da ake gudanarwa wahala ne fiye da yadda aka zata, musamman duba da tsofaffin kayayyakin da ke cikinsu.
Najeriya na da matatu da suka haɗar da na Fatakwal, Warri da Kaduna, sai dai duk suna fama da matsaloli kuma ba sa yin aiki yadda ya kamata.
Tun tuni masana da masu ruwa da tsaki a fannin mai ke bukatar a mika ragamar gudanar da matatun ga kamfanonin masu zaman kansu, domin samar da ingantaccen aiki.
A watan Nuwamba na 2024, NNPCL ya sanar da cewa an fara tace mai a matatar Fatakwal, amma daga bisani aka dakatar da aikin a watan Mayu 2025 saboda wasu matsalolin da suka shafi gyare-gyare.
Har yanzu ana ci gaba da aikin gyaran matatun Warri da Kaduna.