Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta yarda da shirin Amurka na mayar da wasu ƴan ciranin Venezuela zuwa ƙasar ba.
A wata hira da gidan talabijin na Channels, Tuggar ya ce Najeriya na fama da nata matsaloli, don haka ba za ta amince a ɗora mata nauyin wasu ‘yan ƙasashen waje da Amurka ke ƙoƙarin fitarwa daga cikin ta ba.
Wannan mataki na Amurka ya zo ne kwanaki kaɗan bayan ta sanar da sauya tsarin bai wa ƴan Najeriya bizar yawon buɗe ido da kasuwanci, lamarin da gwamnatin Najeriya ta nuna rashin jin daɗi akan sa.
An dade da zargin cewa gwamnatin Amurka, musamman a zamanin Trump, na ƙoƙarin fitar da baƙin haure daga ƙasarta, musamman baƙaƙen fata, tare da neman wata ƙasa ta baƙaƙen fata da za a mayar da su.